Yadda Akayi Jana’izar Jarumin Kannywood, Umar Malumfashi (Kafi Gwamna)

An yi jana’izar fitaccen jarumin Kannywood, Umar Yahaya Malumfashi wanda Allah Ya yi wa rasuwa da yammacin ranar Talata, bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Jarumin wand aka fi sani da Bankaura ko Yakubu ka fi gwamna, na daya daga cikin manyan jaruman masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood da suka shafe shekaru ana damawa da su.

Sai dai wata majiya ta bayyana cewar jarumin ya sa fama da rashin lafiya, kafin Allah ya karbi ransa.

Tuni jarumai da dama ne suka halarci jana’izarsa a gidansa da ke unguwar Hotoro Tsamiyar Boko a Jihar Kano.

Wasu daga cikin jaruman Kannywood da abokai da suka halarci jana’izar.

Leave a Comment