Allah Yayiwa Sani Garba Sk Rasuwa – Fitaccen Jarumin Kannywood

Allah Yayiwa Sani Garba Rasuwa wanda aka fi sani da Sk.

Fitaccen producer Abdul Amart shine wanda ya tabbatar wa da duniya rasuwar jarumin Sani Garba Sk.

Rasuwar Sani Garba Sk – Jarumin Kannywood

Marigayin ya rasu ne a Asibitin Muhammadu Abdullahi Wase da ke Nasarawa a ranar Laraba da yamma.

“Sani SK ya kai kusan shekara uku yana jinya a tsattsaye, amma rashin lafiyar ta taso masa sosai ne a baya-bayan inda ya shafe mako biyar yana jinya a asibitin,” in ji Amart.

Bugu da qari, Abdul Amart ya qara da cewa; Marigayin Sani Garba Sk ya dade yana fama da cutar ciwon suga. Wanda daga bisani ta haifar masa da cututtuka kamar hawan jini da koda da hanta.

Da wannan ne muke miqa sokon Ta’aziya wa iyalansa, da Kannywood da kuma daukakin jama’ar Musulmi.

Allah ya jikansa yayi masa Rahma yasa Aljanna ce makomar sa. AMEEN 🙏🙏


Posted

in

by

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *